Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bayar da rahoto dangane da karfin takarar biranen kasar Sin
2019-06-24 11:21:56        cri

A yau ne cibiyar nazarin ilmin zamantakewar al'umma ta kasar Sin ta fitar da rahoto na 17 dangane da karfin takarar biranen kasar Sin, rahoton ya nuna cewa, Shenzhen da Hongkong da Shanghai da Guangzhou da Beijing da Suzhou da Nanjing da Wuhan da Taibei da kuma Dongguan sun kasance birane 10 dake kan gaba ta fannin ci gaban tattalin arziki a kasar Sin a shekarar 2018.

Rahoton dai ya yi nazari ne a kan biranen kasar Sin kusan 300, ta fannonin ci gaban tattalin arziki da dadin rayuwa da dauwamammen ci gaba da kuma yanayin harkokin kasuwanci.

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa, a nan gaba, birane za su ci gaba da bunkasa, kuma an yi hasashe ya zuwa shekarar 2035, yawan biranen kasar Sin zai kai kaso sama da 70%, kuma karin iyalai a maimakon daidaikun mutane za su kaura daga karkara zuwa biranen kasar. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China