Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana fatan ba za a rufe kofar shawarwari cikin adalci a tsakanin Sin da Amurka ba
2019-06-22 16:19:37        cri
Game da ra'ayin bangare daya da matakan matsawa kamfanonin Sin lamba da kasar Amurka ta aiwatar, wasu wakilan kasashen waje da suka halarci bukukuwan hukumar kula da harkokin cudanya ta jam'iyyar Kwamis ta kasar Sin sun bayyana cewa, kasar Amurka ta janye daga tsarin bangarori daban daban sau da dama, da daga buga harajin kwastam da sauran ayyuka, wadanda ba za su samar mata moriya ba, inda suka yi kira da kada a rufe kofar yin shawarwari cikin adalci tsakanin Sin da Amurka.

Jakadar Mozambique dake kasar Sin Maria Gustava ta nuna damuwa game da takaddamar ciniki dake tsakanin Sin da Amurka. Tana mai cewa, kamar Sin da Amurka suka fi yin ciniki a duniya, takaddamarsu a fannin cinikaya za ta haifar da mummunan tasiri a duniya, musamman ga tattalin arziki da cinikin waje na kasashe masu tasowa.

Shugaban kungiyar ciniki tsakanin Sin da Spaniya Carlos Viles ya ce, kasashen duniya sun nuna goyon baya ga kasar Sin, game da takaddamar ciniki da Amurka ta tada, domin bunkasuwar Sin ta wakilci kyakkyawar makoma. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China