Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya gana da bakin Afrika
2019-06-24 10:49:37        cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi ya gana da takwarorinsa na kasashen Saliyo, Gabon, Kamaru da dai sauransu, wadanda suka halarci taron tabbatar da ci gaban da aka samu a taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika, da aka yi a jiya Lahadi a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar, Mista Wang ya ce, taron wannan karon, ya samu halartar tawagogin manyan wakilan kasashen Afrika 53, ciki har da ministocin harkokin waje na kasashe 25, matakin da ya bayyana yadda kasashen Afrika ke dora muhimmanci sosai kan huldar kut da kut dake tsakaninsu da kasar Sin. Ban da wannan kuma, taron zai zama wasu sabbin damammaki ga bangarorin biyu, wajen kara hadin gwiwarsu bisa sabon yanayin da muke ciki. Mista Wang ya kara da cewa, goyon bayan da Sin ke nunawa kasashen Afrika ta fuskar kudade na bisa tushen adalci da son rai, da zummar taimakawa kasashen Afrika waje daga karfinsu na samun bunkasuwa mai dorewa ta dogaro da kansu. Ya ce, babu tarko iri na basussuka tsakanin bangarorin biyu, Sin ba za ta nemi cimma wani burinta na siyasa ta hanyar yin amfani da wannan batu ba. Sin na tsayawa tsayin daka kan manufar gudanar da harkoki tsakanin kasashe daban-daban da kin yarda da ko wani mataki na kashin kai da babakere. Sin ta dauki wannan mataki ne ba ma kawai tana kiyaye moriyarta da ta dace ba, har ma tana kokarin kiyaye adalcin kasa da kasa da muradun bai daya na kasashe marasa karfi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China