Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Sin ya ce bikin baje-kolin tattalin arziki da kasuwanci na Sin da Afirka zai kunshi fasahohin zamani da dama
2019-06-23 17:01:49        cri
Za'a yi bikin baje-kolin tattalin arziki da kasuwanci na Sin da Afirka karo na farko daga ranar 27 zuwa 29 ga wata a birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin, inda kasar Masar ta zama daya daga cikin kasashe shida da za su nuna al'adunsu na musamman a bikin. Babban jami'in kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na kasar Sin dake kasar Masar Han Bing, ya bayyana cewa, bikin zai baiwa jama'a damar more fasahohin zamani daban-daban, abin da zai taimaka sosai ga hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannonin tattalin arziki da kasuwanci.

Han ya ce, Masar za ta tura wata tawaga mai kunshe da mutane sama da 40 zuwa Changsha, ciki har da ministan yawon shakatawa na kasar, jami'ai daga hukumomin yawon shakatawa da zuba jari da ayyukan gona da kasuwanci da sauransu, gami da wakilai daga shahararrun kamfanonin Masar guda goma, wadanda suka shafi ayyukan gona da sana'ar hannu da hada-hadar kudi da sauransu.

Han ya ci gaba da cewa, bikin baje-kolin na wannan karon ya bambanta da sauran bukukuwa, duba da irin makasudin shirya shi, wato ba kawai za'a yi shawarwarin cinikayya ba ne, har ma za'a shirya wasu nune-nune na musamman, ciki har da nune-nunen al'adun kasashe daban-daban, da bikin nuna kayan Afirka da sauransu.

Han ya ce, hadin-gwiwar Sin da Afirka na dacewa da hadin-gwiwar shawarar "ziri daya da hanya daya", a karkashin wannan shawarar, hadin-gwiwa sassan biyu za ta ci gaba da habaka.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China