Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin ma'aikatar kasuwanci: Ana fatan daidaita takaddamar ciniki a tsanin Sin da Amurka ta hanyar yin shawarwari
2019-05-09 20:27:59        cri
Kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, Sin ba ta amince da yadda Amurka ta dauki matakai na kara sanya haraji ba.

Kakakin ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, yana mai cewa ba wanda zai ci gajiyar yakin ciniki, kuma hakan bai dace da moriyar kasar Sin, da ma ta Amurka ba, da ma duniya baki daya.

Kaza lika kasar Sin na fatan Amurka za ta hada kai da ita, kuma a yi shawarwari a maimakon daukar irin wadannan matakai wajen daidaita takaddamar, ta yadda za a cimma yarjejeniyar cin moriyar juna bisa tushen mutunta juna, da kuma zaman daidaito da juna. A sa'i daya kuma, kasar Sin a shirye take ta kiyaye hakkinta yadda ya kamata. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China