Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping zai kai ziyara a kasar Kyrgyz da ta Tajikistan
2019-06-10 13:37:02        cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gudanar da taron manema labaru a yau, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Zhang Hanhui ya yi bayani game da ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai a kasar Kyrgyz da ta Tajikistan tare da halartar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 19 da kuma taron koli na biyar na hadin gwiwa da yin imani da juna na Asiya.

Zhang Hanhui ya bayyana cewa, a yayin taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, shugaba Xi Jinping zai halarci liyafa da bukukuwa manya da kanana tare da shugabannin kasa da kasa. Shugaba Xi Jinping zai yi musayar ra'ayoyi tare da shugabannin kasa da kasa kan yanayin bunkasuwar kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da makomarta, da kuma manyan batutuwan kasa da kasa da yankuna, da kuma tattauna kan yadda za a dauki matakai don tinkarar kalubale da sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa tare. Ya ce Sin za ta yi kira ga bin tunanin Shanghai, da kara yin imani da hadin gwiwa da juna a kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a fannonin siyasa, da kiyaye tsaro, da tattalin arziki, da al'adu, da mu'amala da juna da sauransu, ta yadda za a iya daga ingancin kungiyar zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China