Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar IRCG ta Iran ta ce ta shirya dakile barazanar yaki daga Amurka
2019-05-20 11:23:31        cri
Babban kwamandan rundunar sojin IRGC ta Iran, Manjo Janar Hossein Salami, ya ce rundunar ta shirya kare kasar daga barazanar yaki daga Amurka.

Wani gidan talabijin na kasar ya ruwaito Manjo Janar Hossein Salami na cewa, Iran na fuskantar barazana a kusa da iyakarta, kuma rundunar IRGC ta shirya kanta don tunkarar barzanar.

Gwamnatin Amurka na nufin kai Iran teburin sulhu ta hanyar matsa mata lamaba. kuma Gwamnatin Iran ta yi ammana cewa Washington na neman cimma sabon yarjejeniyar nukiliya da ita, domin kara dakatar da shirin nukiliyar kasar, da nufin hana ta ci gaba da kera makamai masu linzami da kuma dakile yunkurinta na yin tasiri a yankin.

Har wa yau, ministan harkokin wajen Pakistan, Shah Mehmood Qureshi dake ziyara a kasar Kuwait, ya ce a shirye Pakistan ta ke, ta saukaka rage ta'azzarar zaman dar-dar a yankin da kuma mara baya ga zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shah Mehmood Qureshi, ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Kuwait (KUNA).

Ministan ya ce ya damu da karuwar zaman dar-dar da ake samu tsakanin Amurka da Iran, kuma a ko da yaushe, Pakistan na goyon bayan zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma za ta yi farin cikin taimakawa rage zaman na dar-dar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China