Babu wani jirgin ruwan kasar Iran da ya iya shiga kowace tashar jiragen ruwa ta kasashen waje
Kamfanin dillancin labaru na IRNA na kasar Iran ya bayyana a jiya Lahadi cewa, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya yi jawabi cewa, kasar Amurka tana matsawa kasar Iran lamba sosai, ana sa ido kan dukkan jiragen ruwan jigilar mai na kasar Iran ta tauraron dan Adam na kasar Amurka, har ma babu wani jirgin ruwan kasar Iran da ya iya shiga kowace tashar jiragen ruwa ta kasashen waje. Amma hakan bai nakasa kasar Iran ba. Jama'ar kasar Iran suna hadin kai tare da juna da yin imani da juna, hakan zai taimaka wajen yaki da rikicin tattalin arziki da kasar Amurka ta sanya kasar Iran. Kasar Iran ta shirya isassun kayayyaki, gwamnatin kasar Iran ba za ta sanya jama'arta cikin mawuyacin hali ba. (Zainab)
Labarai masu Nasaba