Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe taron Shangri-la karo na 18
2019-06-03 10:08:19        cri
An rufe taron Shangri-la karo na 18 a Singapore, jiya 2 ga wata, mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin kuma ministan tsaron kasar Wei Fenghe ya halarci taron tare da ba da jawabi mai taken "Hadin kan Sin da duniya ta fuskar tsaro".

A cikin jawabinsa, Mista Wei ya ce, gwamnatin Sin da sojojinta na tsayawa kan tabbatar da zaman lafiya da zaman karko wajen fuskantar sauye-sauyen halin da duniya ke ciki. Ya kamata a mutunta babbar moriyar kasa da kasa da ayyukan da suke mayar da hankalinsu yayin da ake kokarin tabbatar da bunkasuwar yankin Asiya-Pacific. Sin ba za ta kawo cikas ga bunkasuwar sauran kasashe ba, kuma za ta nace ga moriyarta ta fuskar mulkin kai, tsaro da samun bunkasuwa.

Game da batun yankin Taiwan, Mista Wei ya ce, kasar Sin guda daya a duniya da ba wanda zai iya ware ta a ko da yaushe, duk wani yunkuri da za a yi wajen tsoma baki cikin wannan batu zai ci tura, sojojin kasar Sin na da imanin kare kasar.

Yayin da ya tabo maganar dangantakar Sin da Amurka, ya ce, hanyar daya tilo a gaban kasashen biyu ita ce hadin kansu don kawo moriyar juna, a maimakon yin ja-in-ja wanda zai kawo illa garesu. Ya kuma jaddada cewa, ya kamata sojojin kasashen biyu sun tabbatar da matsaya daya da shugabanninsu suka cimma ta yadda dangantakar sojojin za ta ba da tabbaci ga dangantakar kasashen biyu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China