Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shiyyar gabashin kasar Sin za ta gina asibitin ido mai amfani da fasahar 5G
2019-06-03 09:45:55        cri
Za'a gina asibitin ido mai amfani da fasahar 5G a birnin Xiamen, dake lardin Fujian na gabashin kasar Sin domin kyautata rayuwar marasa lafiya.

Asibitin na 5G za'a gina shi ne bisa hadin gwiwa da cibiyar kula da ido na jami'ar Xiamen, da reshen hukumar sadarwa ta kasar Sin dake Xiamen, da kuma babban kamfanin fasahar zamani na Huawei, kamar yadda sanarwar bangarorin uku da suka yi hadin gwiwa suka fitar a ranar Lahadi.

"Fasahar 5G ba wai tana inganta tsarin sadarwa ne kadai ba, har ma tana samar da damammaki ga fannin kiwon lafiya," inji Zhang Guangbin, mataimakin shugaban cibiyar kula da lafiyar ido.

A zamani mai zuwa nan gaba, ana sa ran yin aikin tiyatar ido ta hanyar intanet, da ganawa da likita, da neman shawarwari game da yadda za'a gudanar da aikin tiyatar ido, su ne muhimman bangarorin da fasahar za ta fi mayar da hankali kansu, inji Zhang.

Manyan birane kasar Sin sun fara amfani da fasahar 5G domin biyan muradun al'umma a bangarori da suka shafi sufuri, nishadantarwa da kuma kiwon lafiya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China