Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Peng Liyuan ta gana da daliban ketare masu neman digiri na biyu na kwalejin 'yan mata ta kasar Sin
2019-05-31 10:48:02        cri

Uwargidan shugaban kasar Sin Madam Peng Liyuan ta gana da wasu daliban ketare masu neman digiri na biyu na kwalejin 'yan mata ta kasar Sin a birnin Beijing a jiya Alhamis, don sanin yadda suke zama a nan kasar Sin. Kuma tana fatan daliban za su zama gada da ta hada kasashensu da kasar Sin waje guda bayan sun kammala karatunsu sun koma gidajensu, ta yadda za su ba da gudunmawarsu wajen sa kaimi ga gudanar da harkokin 'yan mata na kasa da kasa da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkanin Bil Adama.

An ba da labari cewa, a gun taron koli na 'yan mata da aka yi a shekarar 2015, shugaba Xi ya sanar da gayyatar 'yan mata dubu 30 daga kasashe masu tasowa don su kara ilmi a kasar Sin. Aikin ba da ilmi na digiri na biyu da kwalejin ya gabatar mai taken "Dangantaka tsakanin karfin jagoranci na mata da bunkasuwar al'umma ", ya kasance matakin da ya tabbatar da wannan buri na shugaba Xi.

A kwanakin baya, wasu dalibai sun mika wata wasika ga shugaba Xi da Madam Peng don bayyana ci gaban da suka samu wajen karatu, da mika godiya gare su da taimakon da Sin ke ba su.

A cikin ganawar da aka yi a wannan rana, Madam Peng ta furta cewa, Sin na dora muhimmanci sosai kan ayyukan mata, kuma tana fatan kara hadin kanta da kasashen duniya don ingiza wannan aiki yadda ya kamata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China