Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNEP: Kasar Sin ta samu ci gaba wajen tsabtace iska
2019-06-03 10:07:04        cri

Madam Jorce Msuya, mukaddashin darektar zartaswa ta hukumar tsara harkokin muhalli ta MDD (UNEP), ta bayyana a kwanakin baya cewa, kasar Sin ta samu ci gaba sosai a fannin tinkarar matsalar gurbacewar iska, kuma ta zame ma sauran kasashe masu tasowa abun koyi.

Kafin haka, yayin babban taron muhalli karo na 4 na MDD wanda ya gudana a watan Maris din bana, tawagar kasar Sin da hukumar UNEP sun sanar da cewa, an ba kasar Sin damar karbar bakuncin bukukuwan ranar muhalli ta duniya na bana. A cewar hukumar UNEP, ta hanyar karbar bakuncin bukukuwan, kasar Sin za ta iya nunawa kasashen duniya dukkan nasarorin da ta samu a kokarin tsabtace muhallin kasar.

A ganin Madam Msuya, dalilin da yasa kasar Sin ta samu wannan ci gaba ya kunshi fannoni guda uku: Na farko, kasar Sin na kokarin wayar da kan jama'arta game da ra'ayin kare muhalli; na biyu, kasar tana daukar takamamman matakai don sa ido kan yadda ake gudanar da aikin kare muhalli, tare da tabbatar da ganin gwamnatoci, da kamfanoni, gami da jama'a, dukkansu su aikata yadda ake bukata; na uku shi ne, an tsara wasu manufofi masu alaka da aikin kare muhalli, inda aka bukaci ma'aikatu masu samar da kayayyaki da su inganta fasahohinsu, da yin amfani da makamashi mai tsabta. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China