![]() |
|
2019-05-24 10:59:00 cri |
Ma Zhaoxu, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron tattaunawa game da bada kariya ga fararen hula a lokacin fama da tashin hankali na masu dauke da makamai. Ya ce, "Yin rigakafin faruwar rikici da warware rikicin ta hanyar lumana su ne muhimman hanyoyi mafiya dacewa wajen baiwa fararen hula kariya."
Ma Zhaoxu ya kara da cewa, ya kamata kwamitin sulhun MDD ya yi cikakken kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa, kana ya kara kaimi wajen warware tashe tashen hankula ta hanyar matakan tattaunawa, da tuntubar juna, da kuma tattaunawar siyasa, domin kubutar da fararen hula daga fadawa cikin yaki.
Jakadan na Sin ya ce, ya kamata kasa da kasa su rungumi cikakken tsari, da hadin gwiwa game tunkarar matsalar tsaro, kuma su hada kai da juna karkashin tsarin tattaunawa, maimakon yin fito-na-fito, da yin abota da juna maimakon rarrabuwar kawuna, domin samar da muhalli mai cikakken yanayin zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China