2019-06-02 12:33:23 cri |
Takardar ta bayyana cewa, cimma wata yarjejeniyar moriyar juna a tsakanin Sin da Amurka, ta dace da muradun kasashen biyu, da ma burin kasa da kasa. Ana fatan kasar Amurka za ta yi hadin gwiwa tare da kasar Sin, da daidaita matsaloli bisa ka'idojin girmama juna da nuna daidaito ga juna, da kara yin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, a kokarin raya dangantakarsu bisa tushen hadin gwiwa da daidaito da ma zaman karko, ta hakan za a amfanawa jama'arsu har na dukkan duniya baki daya. (Zainab)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China