in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gudanar da gyara game da ka'idojin hada hadar zuba jari
2019-03-19 10:55:40 cri

Hukumar dake lura da hada hadar musayar kudade ta kasar Sin SAFE, ta ce an gudanar da gyara game da ka'idar hada hadar zuba jari, ta kamfanonin kasa da kasa masu cinikayya da Sin.

Sabuwar ka'idar dai za ta taimaka, wajen bunkasa damar zuba jari cikin 'yanci, da saukaka hada hadar cinikayya, da zuba jari, tare da samarwa kasar damar bunkasa tattalin arzikin ta.

Bayanan da mahukuntan kasar suna fitar, sun nuna aniyar kasar ta saukaka hanyoyin yin rajistar hada hadar basussukan kasashen ketare, da na rance da kamfanonin ketare ke karba. Za kuma a fitar da tsarin gwaji, wanda zai rage wahalhalun da ake fuskanta, yayin warware batun biyan kudade ga kamfanonin ketare bayan yi musu rajista.

A hannu guda kuma, Sin za ta soke tarnaki da kamfanonin waje ke tunkara, na mu'amala da wasu bankuna da aka kebe. To sai dai kuma yayin da ake aiwatar da wannan manufa, za a ci gaba da karfafa sanya ido, domin kare yiwuwar kwararar kudade ba bisa ka'ida ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China