Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 5 a Najeriya
2019-05-18 15:01:23        cri

Kimanin wasu mutane 5 ne aka hallaka, kana an kone wasu shaguna masu yawa a lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram suka afkawa wani kauye dake jihar Adamawa, a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, wata majiya ce ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Mutane da dama sun samu raunuka a lokacin da mayakan 'yan ta'addan suka kaddamar da hari kan kauyen Shuwa dake kusa da garin Madagali da yammacin ranar Alhamis inda suka shafe kusan sa'o'i uku, wani babban jami'in soja ne ya bayyana hakan ta wayar tarho.

Maharan sun kutsa cikin kauye ne da motoci kirar fikof makare da bindigogin dake kakkabo jiragen sama da Babura, inda suka kai harin da nufin kwasar kayan abinci, in ji jami'in sojojin wanda ya bukaci a sakaye sunansa saboda ba a ba shi izinin magana da 'yan jarida game da harin ba.

Wani mazaunin kauyen mai suna James ya ce, maharan sun yi ta harbi kan dukkan mutanen da suka yi ido biyu da su a kauyen, lamarin da ya sa tsoffi da kananan yara da marasa lafiya suka dinga gudu don tsira da rayuwarsu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China