Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan Boko Haram sun kashe masunta 10 a Najeriya
2019-05-18 15:23:14        cri

A kalla gawarwaki masunta 10 ne aka tsinta a ranar Juma'a wadanda ake zaton mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram ne suka hallaka a kusa da birnin Maiduguri dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, in ji wani jami'in hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar.

An kaddamar da harin kan gungun masuntan ne a ranar Alhamis a madatsar ruwa ta Alou Dam, dake da tazarar kilomita 4 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Bello Danbatta, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na jihar Borno, ya ce mafiya yawan masuntan sun fito ne daga kauyen Konduga.

Masuntan suna kan hanyarsu ne zuwa wajen sana'arsu a daidai lokacin da maharan suka afka musu, inda suka hallaka su da kuma jikkata wasu da dama.

A baya bayan nan, mayakan Boko Haram sun sha kaddamar da hare hare kan masunta da manoma a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, inda suke zargin su da samar da bayanai ga jami'an sojoji game da ayyukan ta'addancin da mayakan ke shiryawa.

Ayyukan noma da kamun kifi sun gagari mutane a Maiduguri da kewayenta, sakamakon fargabar da suke nunawa game hare haren mayakan kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China