Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci Afrika ta mayar da hankali wajen raya gandun daji
2019-05-26 16:27:06        cri
MDD ta bukaci gwamnatocin kasashen Afrika da su bada fifiko wajen raya gandun daji a cikin ajandarsu ta raya cigaba.

Peter Gondo, jami'in shiyyar Afrika a taron dandalin MDD game da batun raya gandun daji, yace rashin bada cikakken fifiko a fannin shi ne ya haifar da koma baya, lamarin da ke haddasa karancin samun kudaden shiga a wannan fannin.

Gondo ya danganta rashin samar da isassun kudade shine ke hana kwararru samun damar tsara muhimman ayyukan da zasu bunkasa fannin gandun daji da rashin sanin muhimman bayanan da ake bukata wadanda zasu taimaka wajen raya gandun daji.

Yayi kira ga gwamnatoci dasu gabatar da jerin ayyuka na bangarori masu yawa maimakon gabatar da ayyuka na bangare guda kamar bangaren ruwa, makamashi, aikin gona, da yawon shakatawa.

Jami'in ya lura da cewa raya gandun daji yana iya bunkasa tattalin arzikin kasa amma idan an baiwa fannin fifiko.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China