![]() |
|
2019-05-28 21:40:46 cri |
A nasa bangare, Mahamadou Issoufou ya ce, shawarar "ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping ya bayar ta bayyana manufar samun moriyar juna tare, shawara ce da za ta samar da alfanu ga duk duniya baki daya. Kasashen Afirka sun yabawa manufofin gwamnatin kasar Sin na raya dangantaka tare da Afirka, tare kuma da godewa wasu manyan matakai takwas da Xi Jinping ya sanar a fannin inganta hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Ya ce kasarsa wato Jamhuriyar Nijar ta dade tana martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, da goyon-bayan cimma burin raya kyakkyawar makomar al'umma ta bai daya, haka kuma tana matukar son shiga cikin ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya".
Bayan ganawarsu, shugabannin biyu sun kuma kalli bikin daddale wasu yarjeniyoyin hadin-gwiwa da aka kulla tsakanin Sin da Nijar.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China