Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada bukatar inganta ilimin jami'an sojoji don kara karfin rundunar sojojin kasar
2019-05-22 10:37:02        cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya jaddada muhimmancin inganta ilimin jami'an sojoji, ta yadda za a gina rundunar sojoji mai cike da karfi. Shugaba Xi ya bayyana hakan ne, yayin da ya kai ziyarar gani da ido kwalejin sojoji dake sarrafa makaman yaki ta rundunar sojojin 'yantar da al'ummar kasar Sin a Lardin Jiangxi dake gabashin kasar.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban kwamitin tsakiya na aikin soja na kasar, ya bayyana cewa, ya kamata tsarin ilimin sojoji ya cimma ka'idojin da ake bukata na shiga aikin, da bukatar rundunar sojojin da ma ta ayyukan sojojin da ake bukata nan gaba.

Ya kuma shaidawa makarantu da malaman dake koyar da sojojin, da su koyi dabaru na siyasa, da sanin yadda suka dosa, da zurfafa gyare-gyare da kara ingancin ilimi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China