Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya mika wasikar murnar bude taron samar da hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2019
2019-05-28 14:51:50        cri
An bude taron samar da hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2019 a nan birnin Beijing a yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika wasikar murnar bude taron.

A cikin wasikar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tare da yin kokarin sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, da samar da hidimomi ya kasance muhimmin kashi na cinikin dake tsakanin kasa da kasa da na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, wanda ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Ana da kyakkyawar makoma a wannan fanni, ya kamata a rike wannan dama don samar da kyakkyawar makoma ta samar da hidima a duniya da samun moriyar juna tare.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta yi kokarin sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje da nuna goyon baya ga tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, za a fadada kasuwar jarin waje da kuma samar da yanayin ciniki mai inganci. Sin tana son kara zuba jari da yin hadin gwiwa a fannin samar da hidima a tsakaninta da kasa da kasa, da samar da sauki da yanci ga ciniki da zuba jari, wanda hakan zai sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya mai bude kofa da daidaito da samun moriyar juna. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China