Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga bikin EXPO na masana'antun samar da manyan bayanai na kasa da kasa
2019-05-26 17:05:34        cri
An kaddamar da bikin bajekolin masana'antun samar da manyan bayanai na kasa da kasa na bana a yau Lahadi a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda shugaban kasa Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bude bikin.

Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu fasahohin sadarwar zamani na bunkasuwa cikin sauri, musamman fasahohin Intanet da masana'antun samar da manyan bayanai gami da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, wadanda ke yin babban tasiri ga ci gaban tattalin arziki da bunkasuwar zaman rayuwar al'ummar kasa da kasa. Kamata ya yi kasashen duniya su karfafa hadin-gwiwa da zurfafa mu'amala, don shawo kan kalubaloli a fannonin da suka shafi doka da tsaro da mulki yayin da ake kokarin raya masana'antun samar da manyan bayanai.

Xi ya kuma jaddada cewa, kasar Sin na maida hankali sosai kan raya masana'antun samar da manyan bayanai, tana kuma fatan yin kokari tare da sauran kasashe don lalibo sabuwar hanyar samun bunkasuwa a bangaren fasahohin sadarwar zamani.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China