Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Baje kolin Suga na kasar Sin ya ja hankalin kamfanoni 800 na fadin duniya
2019-05-27 10:23:48        cri
Baje kolin suga na kasar Sin na bana, wanda aka kammala da yammacin jiya Lahadi a Nanning, babban birnin yankin Guangxi Zhuang mai cin gashin kansa dake kudu maso yammacin kasar Sin, ya ja hankalin kamfanoni sama da 800 daga fadin duniya.

Sama da mahalarta 30,000 daga fadin duniya, ciki har da kwararru da 'yan kasuwa na masana'antar suga ne suka halarci baje kolin na yini 3, inda aka baje nau'ikan kayayyakin suga sama da 100 a wurin mai fadin muraba'in mita 30,000.

Yayin baje kolin, birnin Chongzuo da aka fi sani da babban birnin suga na kasar Sin, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar ayyuka 13 da darajarsu ta kai yuan biliyan 10.8, kwatankwacin dala biliyan 1.57.

An kuma gudanar da babban taron suga na duniya a birnin, inda shugabanni da kwararru daga hukumar bunkasa cinikin suga ta kasa da kasa, da kungiyar sarrafa rake ta kasar Brazil, da kamfanin samar da suga na Indiya, da sauran kamfanoni da cibiyoyi na fadin duniya suka tattauna tare da lalubo hanyoyin raya masana'antar.

A yankin Guangxi Zhuang mai cin gashin kai dake zaman yankin kasar Sin da ya fi samar da suga ake samar da kaso 60 na sugan kasar. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China