![]() |
|
2019-05-27 13:34:10 cri |
Shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou ya isa birnin Hangzhou na lardin Zhejiang na kasar Sin a jiya Lahadi, a ziyarar aiki da ya fara a kasar Sin. A wannan rana, shugaba Issoufou da tawagarsa sun kai ziyara a cibiyar kamfanin Alibaba dake birnin Hangzhou.
Shugaba Issoufou ya bayyana cewa, kasarsa ta Nijer tana son samun ci gaba a yayin da ake yin kwaskwarima kan sabbin fasahohi na sabon zagaye, don haka ta kara zuba jari ga ayyukan more rayuwa, musamman a fannin yanar gizo, da yunkurin yin amfani da yanar gizo a birane da kauyuka na kasar. Shugaba Issoufou yana fatan za a yi amfani da dandalin kamfanin Alibaba na yanar gizo don fitar da kayayyakin musamman na kasar Nijer zuwa kasashen waje. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China