Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kara inganta matakan kula da yara a yankuna masu fama da talauci
2019-05-27 20:37:43        cri
Rahotanni daga kasar Sin na cewa, gwamnatin kasar ta kara karfafa matakan ba da kariya ga yaran da iyayensu suka bar su a kauyuka, suka kaura zuwa birane don aiki ko wadanda ke zaune a yaukuna masu fama da talauci, yayin da kasar ke yaki da talauci.

Mataimakin darekta a sashen kula da walwalar yara a ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar, Ni Chunxia ya shaidawa taron manema labarai cewa, a shekarar 2019 da muke ciki, a karon farko ma'aikatar ta kebe Yuan miliyan 400, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 58, daga asusun tallafawa mutane dake fama da matsalar kudi, domin kula da wadannan yara.

Ni ya ce, za a yi amfani da asusun ne wajen tattara shaidu kan wadanda ke neman taimako,tantance yadda ake kula da yaran, da sake bibbiyar wadannan yara da ziyartar yaran dake bukatar taimako, musamman wadanda ke zaune a yankuna masu fama da talauci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China