Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Burkina Faso tana maida hankali ga dangantakar sada zumunta a tsakaninta da kasar Sin
2019-05-27 13:48:05        cri
Ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso Alpha Barry, ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasarsa ta Burkina Faso ta tsaya tsayin daka kan ka'idar Sin daya tak, da maida hankali sosai ga dangantakar sada zumunta a tsakaninta da kasar Sin da aka sake kullawa.

Ofishin jakadancin Sin dake kasar Burkina Faso ya gudanar da bikin murnar cika shekara daya da sake kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Burkina Faso da bikin nune-nunen hotuna kan nasarorin da kasashen biyu suka samu a birnin Ouagadougou dake kasar Burkina Faso a wannan rana, inda minista Barry ya bayyana cewa, a cikin shekara daya da aka sake kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, Sin ta maida hankali ga bukatun kasar Burkina Faso, da samar da gudummawa sosai wajen sa kaimi ga samun ci gaba a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma tsaron yankin. Sake kulla dangantakar dake tsakaninsu ya dace da moriyar jama'arsu da yanayin da ake ciki. Kasar Burkina Faso za ta yi kokari tare da kasar Sin wajen inganta hadin gwiwarsu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare, jakadan Sin dake kasar Burkina Faso Li Jian, ya bayyana cewa, Sin tana son more fasahohin raya kasa tare da kasar Burkina Faso, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu, don taimakawa kasar Burkina Faso wajen neman hanyar samun ci gaba mai dacewa da samun bunkasuwa mai dorewa yadda ya kamata. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China