![]() |
|
2019-05-27 10:11:25 cri |
Rahoton da kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin ta fitar tare da wasu bangarori, ya ce cinikin motocin jigilar fasinjoji zai kai kimanin miliyan 23.7, adadin da ya yi kunnen doki da na bara.
Daga cikin jimilar, cinikin motoci masu amfani da makamshi mai tsafta zai karu zuwa miliyan 1.6 a bana, daga miliyan 1.26 a 2018, adadin da ya karu da kimanin kaso 27.
Duk da cewa cinikin motocin ya sauka da kaso 2.8 zuwa miliyan 28.08 a bara, Kasar Sin ce ta mamaye kaso 30.6 na kasuwar motoci ta duniya.
Zuwa karshen bara, kasar Sin ce ke kan gaba a fannin sayar da motoci a duniya, matsayin da ta rike shekaru 10 a jere.
Yawan cinikin motoci masu amfani da sabon makamashi ya karu da kaso 61.7 zuwa miliyan 1.26 a bara, biyo bayan wasu kyawawan dabarun gwamnati, adadin da ya dauki kaso 60 na cinikin irin motocin a duniya. (Fa'iza Msutapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China