Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan tsaron Somalia ya jinjinawa kwazon tawagar AMISOM
2019-05-27 09:36:41        cri
Ministan tsaron kasar Somalia Hassan Ali Mohamed, ya jinjinawa kwazon tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar AU a kasar sa ko AMISOM a takaice, yana mai cewa tawagar ta yi rawar gani, wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar dake kahon Afirka.

Wata sanarwa da ofishin AMISOM din ya fitar a jiya Lahadi, ta rawaito Hassan Ali Mohamed na cewa, AMISOM ta dakile mummunan tasirin yakin basasa da ya dade yana addabar Somalia, wanda kuma ya raba dubban al'ummar ta da muhallan su.

Ministan ya ce daya daga manyan dalilan kafa kungiyar AU, shi ne ba da tallafin ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen Afirka da al'ummun su. Don haka a cewar sa, AMISOM ta zamo wani misali na irin gajiyar da kasashe mambobin AU ke ci daga kungiyar.

Jami'in ya yi tsokacin ne yayin da yake jawabi, a taron ranar Afirka da ta gudana a birnin Mogadishu fadar mulkin Somalia, yana mai cewa, kudurorin kungiyar AMISOM, sun dace da muradun wadanda suka yi hidimar kafa kungiyar hadin kan Afirka, wadda a baya ake kira OAU.

Ya ce ainihin kudurin kafa OAU shi ne 'yantar da Afirka daga Turawan mulkin mallaka, da kare ikon mulkin kai, da martaba hakkin bil Adama, tare da dawo da mutuncin nahiyar baki daya.

Daga nan sai ya sake jinjinawa AMISOM da jami'an ta, bisa kwazon su na tallafawa nahiyar Afirka a fannin wanzar da tsaro, da cimma daidaito, tare da tabbatar da yanayi na lumana a Somalia, yana mai yaba sadaukarwar dakarun tawagar.

Kaza lika ya jaddada bukatar dake akwai ga kasashen nahiyar Afirka, da su taimaka wajen ganin an warware matsalolin 'yan gudun hijira, da masu neman mafaka a cikin kasashen su, ko a kai ga dakile mawuyacin hali da matasan nahiyar ke shiga a kokarin su na tsallakawa nahiyar Turai.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China