Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru: maganar a ce wai Amurka tana hasara a cinikayyar da take yi da Sin, bai ma taso ba.
2019-05-23 14:57:45        cri

Maganganu da aka cewa, wai wagegen gibin cinikayya dake tsakanin kasashen Sin da Amurka shi ya jefa Amurka cikin hasara, har ma ta rasa guraban ayyukan yi sama da miliyan daya a sana'ar kere-kere, wasu kwararrun kasar Sin a fannonin nazarin cinikayya da tattalin arziki daga manyan fannoni sun bayyana a jiya Laraba cewa, kasashen biyu na samun moriyar juna da nasara tare a fannin cinikayyar dake tsakaninsu, maganar a ce wai Amurka tana hasara a cinikayyar da take yi da Sin, bai ma taso ba, matakin Amurka na amfani da batun sanya haraji zai kawo illa ga sauran kasashe da ma ita kanta.

A cikin shekaru sama da 40 da suka gabata, karuwar cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Amurka ta ninka sau 230 da wani abu. Shugaban girmamawa na cibiyar nazarin raya kasa ta jami'ar Peking Justin Yifu Lin ya bayyana a dandalin tattaunawa na CCER da aka shirya a jiya Laraba, cewa kasar Amurka tana sayen kayayyaki daga kasar Sin ne ba domin mutunta kasar Sin ba, cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu cinikayya ce ta samu moriyar juna da nasara tare. Ya ce,

"Kasar Amurka na sayen kayayyaki daga kasar Sin ne saboda ba ta kera irin wadannan kayayyaki, kuma wadannan kayayyakin kirar kasar Sin suna da araha da kuma inganci. Ga misali, kasar Amurka na da karfin kera tufaffi da takalman fatar dabbobi, amma idan ta kera irin wadannan kayayyaki da kanta, to za ta kashe kudi da yawa, jama'arta ma za ma su kashe kudi masu yawa wajen saya. Bisa wannan halin da ake ciki, idan ta shigo da wadannan kayayyaki, za ta biya kudi kadan don sayen kayayyaki masu inganci. Wannan ita ce babbar manufar yin cinikayya, wadanda ba su fahimci tattalin arziki ba, ba za su gane haka ba."

A hakika, kasar Amurka ta ci babbar moriya daga cinikayyar dake tsakaninta da kasar Sin. Bisa nazarin da kwamitin kasa dake kula da harkokin cinikayya a tsakanin Amurka da Sin ya yi, ya nuna cewa, cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu tana taimakawa iyalan Amurkawa wajen rage kudin da suke kashewa na rayuwarsu ta yau da kullum da kimanin dala 850, kwatankwacin kashi 1.5 cikin dari na kudin shigar da suke samu a ko wace shekara. Don haka ana iya cewa, ba kamar wasu Amurkawa dake cewa wai sai dai kasar Sin ta samu moriya, Amurka ce ta yi harasa.

Kwararrun sun kuma nuna cewa, sakamakon bambancin matsayin ci gaban tattalin arziki na kasashen biyu, kasashen Sin da Amurka ma na da bambancin matsayin rarraba ayyuka a jerin sana'o'i a duniya. Kasar Amurka ce a kan gaba a jerin sana'o'i, don haka take samun yawancin moriya a wannan fannin. Babban mai nazari na cibiyar nazarin dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ta jami'ar Tsinghua Zhou Shijian yana ganin cewa, an samu gibin cinikayya ne a tsakanin Sin da Amurka sakamakon yanayin da suke ciki. A cewarsa,

"Halin musamman na kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa shi ne, suna da araha da inganci, musamman ma kayayyakin na yau da kullum masu yawa. Yawan kayan wasa da kasar Amurka ke shigarwa kasarta daga kasar Sin ya kai kashi 86 cikin dari na daukacin irin kayan da take shigowa da su, yawan jakunkunan yawon shakatawa da na safara ya wuce kashi 60 cikin dari, yawan kayan amfanin gida ya kai 44 cikin dari, yawan tufaffin sakawa ya kai 37 cikin dari, yawan kayayyakin injuna da na lantarki ya kai kashi 21 cikin dari, yayin da yawan na'urorin daukar hoto na zamani ya kai 40 cikin dari, yawan kwamfutocin tafi da gidanka ya kai kashi 94 cikin dari. An gano cewa, kasar Amurka na dogaro sosai kan kasar Sin wajen kayayyakin yau da kullum, kuma da kyar a samu wadda za ta maye gurbinta."

Kwararrun sun kuma nuna cewa, ba kasar Sin ba ce ta haddasa babban gibin cinikayya da kasar Amurka ta samu, babban dalilin shi ne, sayen kayayyaki fiye da kima, rashin ajiye kudin ko ta kwana da kuma yawan gibin kudi da take fuskanta.

Shugaban girmamawa na cibiyar nazarin batun raya kasa ta jami'ar Peking Justin Lin ya bayyana, matakin da kasar Amurka ta dauka na kara sanya harajin kwastan kan wasu kasashe da yankuna, ciki har da Sin, Canada, Turai da Japan da dai sauransu, ba zai warware matsalar gibin cinikayya ba, a maimakon haka, jama'arta ce za su yi hasara wajen sayen kayayyaki. Ya ce,

"Alkaluman kididdigar shekarar 2018 na nuna cewa, ko da yake Donald Trump ya dauki wannan babban mataki na kara sanya haraji, amma gibin cinikayyar da kasarsa ta samu ya karu da kashi 12.1 cikin dari, amma ba raguwa ba. Gibin cinikayyar da ta samu kan kasar Sin ya karu da kashi 11.7 cikin dari, lallai ba a warware matsalar da Amurka ke fuskanta ba, a maimakon haka ma, yanayan cinikayyar kasar ne ya tabarbare." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China