![]() |
|
2019-05-20 14:23:09 cri |
A karni na 21, yankin Bayan Ovoo ya yi amfani da albarkatun duwatsu da kogi da tebki da yake da su wajen raya sha'anin yawon shakatawa. Hakan ya kara kudin shiga da mazaunan yankin ke samu, da kuma kara inganta yanayin kauyukan tare da samar da ayyukan yi kimanin 200.
Tun bayan da aka kafa kauyen yawon shakatawa na Bayan Ovoo a hukunce a shekarar 2017, yawan kudin shiga da kowane dan kauyen ke samu ya karu da dubu 2 a cikin shekaru biyu a jere. A shekarar 2018, yawan masu yawon shakatawa da suka ziyarci a kauyen ya kai fiye da dubu 200, yawan kudin shiga da aka samu daga fannonin tikitin wuraren yawon shakatawa, wasanni, abinci da sauran hidimomin yawon shakatawa ya kai Yuan miliyan 2 da dubu 200. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China