in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar UNWTO ta bayyana rawar da kasar Sin ke takawa ga ci gaban yawon bude ido a duniya
2018-08-28 10:08:39 cri
Hukumar kula da harkokin yawon bude ido ta MDD UNWTO, ta ce kasar Sin na ci gaba da jagoran tafiye-tafiyen bude ido a duniya.

Rahoton da hukumar ta fitar jiya mai taken 'Bayanin yawon bude ido na hukumar UNWTO na 2018' ya ce 'yan kasar Sin sun kashe dala biliyan 258 kan yawon bude ido a kasashen waje a shekarar 2017, adadin da ya kai kusan 1 bisa 5 na jimilar abun da ake kashewa na yawon bude ido a duniya.

A cewar rahoton, yawon bude ido a kasashen waje ya karu da kaso 7 zuwa miliyan 1,323 a bara, karuwa mafi yawa da aka samu tun daga shekarar 2010.

Karuwar tafiye-tafiyen ya haifar da karuwar fitar kayayyaki daga kasashe ta hanyar yawon bude ido, inda darajarsa ta kai dala triliyan 1.6 a bara.

Hukumar UNWTO, ta yi bayanin cewa, sakamakon na shekarar 2017 ya samu ne daga dorewar bukatun tafiye-tafiye a fadin duniya, ciki har da farfadowar wuraren da a baya ke fuskantar kalubalen tsaro a shekarun baya-bayan nan.

Har ila yau, hukumar ta bayyana yadda farfadowar tattalin arzikin kasashe kamar su Brazil da Rasha, suka amfana da wuraren da suka ci gaba da kuma masu tasowa.

Har yanzu, Faransa ce ke kan gaba cikin wuraren da ake fi zuwa yawon bude ido, inda Spaniya ke rufa mata baya, yayin da Japan kuma ta shiga cikin jerin kasashe 10 da ake zuwa yawon bude ido, bayan ta shafe shekaru 6 a jere tana samun karuwa a fannin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China