in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afirka da su sassauta matakansu na ba da takardun Visa
2019-05-05 15:48:35 cri
Shugaba Cryril Ramaphosa na kasar Afirka ta kudu, ya bukaci kasashen Afirka da su inganta matakansu na ba da takardun iznin shiga kasashensu, don kara janyo masu yawon shakatawa.

Shugaba Ramaphona wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron tafiye-tafiye mai suna Afirka Indada 2019, wato taron nune-nunen tafiye-tafiye mafi girma na nahiyar da ya gudana a birnin Durban dake gabashin kasar, ya ce, wajibi ne kasashen Afika, su kawar da tarkin da masu sha'awar kawo ziyara kasashen Afirka ke fuskanta.

Ya ce, yanzu haka sun himmatu wajen ganin an cimma nasarar manufar kungiyar AU ta yin tafiye-tafiye a kasashen nahiyar ba tare da takardar Visa ba, da ma samar da kasuwar sufurin sama guda daya tilo ta Afirka.

Shugaban ya kara da cewa, kasarsa tana mayar da hankali wajen inganta sassan dake bukatar kwadago, kamar aikin gona, tattalin arzikin teku da yawon bude ido, a wani mataki na farfado da tattalin arzikinta

Bikin na kwanaki uku, wanda aka bude a ranar Alhamis din da ta gabata, ya janyo daruruwan wakilai daga sassan nahiyar da ma sauran kasashe, inda za su zakulo hanyoyin bunkasa bangaren yawon ido a Afirka. Bugu da kari, bikin ya samar da wata dama ta nuna kayayyakin yawon bude ido da Allah ya horewa sassan nahiyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China