Sanarwar ta kara da cewa, tun a watan Yunin bana, sassa kasar ke fama da ambaliyar ruwa sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya da ake ta shekawa. Yankunan da suka fi fama da bala'in sun hada da jihohin Agadez, Maradi, Zinder, da kuma Diffa. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, ban da hallaka mutane, matsalar ta kuma haddasa lalacewar wasu gidaje fiye da 7200, da gonakin da fadinsu ya kai kadada 8162 da ruwa ya malale. (Bello Wang)