Karamin sakatare mai kula da shirin ci gaba mai dorewa na kasar Morocco Nezha El Oufi da ministan muhalli da raya birane da shirin ci gaba mai dorewa na Jamhuriyar Nijar Almoustapha Garba ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin kasashensu.
Bangarorin biyu sun kuma amince su aiwatar da ayyukan da suka cimma a tsakaninsu, musamman a bangaren hadin gwiwar kasa da kasa. (Ibrahim)