Wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Laraba ta nuna cewa, bakin hauren sun tashi ne daga birnin Algiers zuwa lardin Tamanrasset dake kan iyakar Nijar da kasar Mali. Wata tawagar hukumar mai kunshe da likitoci daban-daban da masana tunanin dan-Adam ne ta yiwa ayarin masu ba da agajin jin kai dake kula da aikin mayar da bakin hauren rakiya.
Sanarwar ta bayyana cewa, kafofin watsa labarai na gida da na ketare sun kalli shirin mayar da bakin hauren zuwa kasashensu na asali, wanda ya kuma samu halartar masu sa–ido daga hukumomin MDD dake kasar Aljeriya, kamar babbar hukumar kula da 'yan gudun hijira da hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya.(Ibrahim)