in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar cutar tabin hankali na da nasaba da karancin bitamin D da jarirai sabbin haihuwa suka yi fama da ita
2020-07-02 08:24:06 cri

Wani sabon nazari da masu nazari daga kasashen Austrlia da Denmark suka gudanar cikin hadin gwiwa ya nuna cewa, idan jarirai sabbin haihuwa su ka yi karancin bitamin D, za su kara fuskantar barazanar kamuwa da cutar tabin hankali yayin da suka balaga. Masu nazarin suna ganin cewa, mai yiwuwa da masu juna biyu sun sha isasshen bitamin D, watakila, hakan na iya rage wannan barazana.

Masu nazarin sun gudanar da nazarin kan 'yan kasar Denmark fiye da dubu 2 wadanda aka haife su daga shekarar 1981 zuwa 2000, inda suka tantancen yawan bitamin D da ke cikin jininsu yayin da aka haife su, sun kuma kwatanta yawan bitamin D da ke cikin jinin mutanen da suka kamu da matsalar tabin hankali da kuma mutanen da suke da koshin lafiya bayan da suka balaga.

Masu nazarin sun gano cewa, akwai wata alaka a tsakanin matsalar karancin bitamin D cikin jinin jarirai sabbin haihuwa da kuma barazanar kamuwa da matsalar tabin hankali bayan da suka balaga.In an kwatanta su da jarirai sabbin haihuwa wadanda suke da koshin lafiya, jarirai sabbin haihuwa wadanda suke da karancin bitamin D a jininsu sun fi fuskantar barazanar kamuwa da matsalar tabin hankali bayan da suka balaga, har da kaso 40 cikin dari.

Cutar tabin hankali, wani nau'in ciwo ce da kwakwalwar mutane ba ta aiki yadda ya kamata.Wadanda suke fama da wannan lalura, su kan ga abubuwan da babu su a zahiri, suna rudewa, kuma suna matsalar koyo da adana ko tuna muhimman abubuwa. Ya zuwa yanzu ba a san dalilin da ya sa haka ba tukuna.

'Yan tayin da ke cikin masu juna biyu suna dogaro da bitamin D da ke cikin jikin masu juna biyun.Masu nazarin suna ganin cewa, idan masu juna biyu sun sha isasshen bitamin D, to, barazanar da 'ya'yansu suke fuskanta wajen kamuwa da matsalar tabin hankali bayan da suka balaga za ta ragu.

Masu nazarin sun ci gaba da cewa, nan gaba za su gudanar da nazarinsu kan masu juna biyu, don kara sanin yadda shan isasshen bitamin D zai yi tasiri kan kwakwalwar 'yan tayi, yadda za a rage barazanar kamuwa da matsalar tabin hankali da dai sauransu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China