in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a makara da motsa jiki!
2020-05-05 08:30:34 cri

Jami'ar Birmingham ta kasar Birtaniya ta kaddamar da wani sabon nazari a kwanan baya, inda aka nuna cewa, duk da wasu ba safai su kan motsa jiki kullum a baya, amma idan sun fara motsa jiki yayin da suka tsufa, kwarewarsu a fannin inganta karfin jijiyoyinsu ta yi daidai da takwarorinsu wadanda su kan motsa jiki kullum. Lamarin ya shaida cewa, ba a Makara da motsa jiki!

Masu nazari daga jami'ar Birmingham ta kasar Birtaniya sun kwatanta da kuma tantance yadda tsoffafi maza cikin rukunoni guda 2 suka motsa jikinsu. A cikin rukuni na A, tsoffi maza da shekarunsu suka wuce 70 amma ba su kai 90 a duniya ba sun kwashe shekaru da dama suna motsa jiki a kai a kai. A cikin rukuni na B kuma, tsoffi maza da shekarunsu ya yi daidai da takwarorinsu na rukuni na A, amma ba safai su kan motsa jiki ba a baya. Masu nazarin sun bukace su duka da su motsa jiki cikin wani lokaci, sa'an nan ta hanyar kimiyya suka tantance yadda motsa jiki ya kara karfin jijiyoyinsu.

Masu nazarin sun gano cewa, da ma sun yi tsammanin cewa, tsoffin mata da ke cikin rukuni na A, sun kwashe shekaru da dama suna motsa jiki a kai a kai, tabbas jikunansu suna kasancewa cikin koshin lafiya, haka kuma motsa jiki ya inganta karfin jijiyoyinsu kamar yadda ake zato. Amma sakamakon tantancewar ya shaida cewa, ba haka ba ne! Kwarewar wadannan tsoffi maza a cikin rukunoni guda 2 ta kusan yin daidai a wannan fanni.

Masu nazarin na Birtaniya da suka gudanar da nazarin sun yi karin bayani da cewa, wajibi ne a kyautata tsara manufa na gari ta ba da jagora ga al'umma wajen kiwon lafiya, a kokarin ilmantar da al'umma cewa, duk da ba su motsa jiki a dakin motsa jiki ba, idan sun dan motsa jiki a zaman rayuwarsu ta yau da kullum, alal misali, yin aikin lambu, hawa matakala a maimakon shiga cikin lift da dai sauransu, dukkansu za su taimaka wajen inganta karfin jijiyoyinsu.

Dangane da lamarin Zhang Chuji, wata likita da ke aikin a asibitin Tiantan na Beijing ta gaya mana cewa, duk da a baya ba safai akan ku kan motsa jiki ba, amma ba a makara da motsa jiki! Motsa jiki yana amfanawa lafiyarku a ko da yaushe!(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China