in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Motsa jiki yana iya rage barazanar mutuwa sakamakon ciwon hanta
2020-05-05 08:32:59 cri

Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya nuna mana cewa, motsa jiki ta ko wace hanya yana iya rage barazanar mutuwa sakamakon ciwon hanta da ciwon sankarar hanta.

A yayin taron shekarar-shekara dangane da cututtukan kayayyakin jiki masu narka abinci da likitocin ilmin cututtukan kayayyakin jiki masu narka abinci na kasar Amurka suka gudanar, masu nazari sun kaddamar da wannan sakamakon nazari. Masu nazari da suka fito daga jami'ar Harvard ta kasar Amurka sun yi bayani da cewa, nazarinsu ya gano cewa, ko yin tattaki, ko kuma inganta karfin jijiyoyi, dukkansu suna da nasaba da raguwar babbar barazanar mutuwa sakamakon ciwon hanta.

Masu nazarin sun gudanar da nazarinsu kan baligai mata dubu 68 da 449 da kuma baligai maza dubu 48 da 748, inda suka bukace su da su rubuta yadda suke motsa jiki filla-filla, sa'an nan masu nazarin suka tattara bayanan a ko wadanne shekaru 2 daga shekarar 1986 zuwa ta 2012.

Masu nazarin sun tantance bayanan da suka samu, sun gano cewa, a fannin barazanar mutuwa sakamakon ciwon hanta, idan wasu su kan yi tattaki kullum, barazanar da suke fuskanta ta ragu da kaso 73 cikin dari, in an kwatanta su da wadanda ba safai su kan yi tattaki ba. Har ila yau kuma, idan wasu su kan yi tattaki, tare da inganta karfin jijiyoyinsu, to barazanar da suke fuskanta za ta kara raguwa.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, motsa jiki yana amfanawa kiwon lafiyar dan Adam, wannan ba wani sabon tunani bane. Amma a baya ba a gudanar da wani babban nazari kan mutane masu yawan hakan don kara sanin tasirin da motsa jiki ke yi kan raguwar barazanar mutuwa sakamakon ciwon hanta da ciwon sankarar hanta ba.

Masu nazarin sun yi fatan cewa, sakamakon nazarinsu zai taimakawa wadanda suke fuskantar barazanar kamuwa da ciwon hanta wajen tsara shirin motsa jiki filla-filla, ta haka za su samu hanya mafi dacewa gare su wajen motsa jiki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Ba a makara da motsa jiki! 2020-05-05 08:30:34
v Yi hira da likita Adamu Muhammad Sarki(2) 2020-05-05 08:27:25
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China