in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a kula da tsoffi da masu juna biyu da kuma matan da suka haihu ba da dadewa sosai ba
2019-06-24 10:12:00 cri

Sakamakon sauyawar salon zaman rayuwa, ya sa ake kara fuskantar matsin lamba a rayuwa da kuma ayyuka, ciwon bakin ciki ya zama abun da tilas ne mu mai da hankali a kansa. Masana sun yi nuni da cewa, kamata ya yi a kara kulawa da tsoffafi, masu juna biyu da matan da suka haihu ba da dadewa ba, wadanda suke fama da ciwon bakin ciki.

Shugaban asibitin kula da cututtukan tunani na Anding na Beijing mista Wang Gang ya bayyana wa manema labaru a kwanakin baya cewa, ga tsoffafi, a yawancin lokuta, ciwon bakin ciki ya zama wata alama ta kamuwa da ciwon tsananin mantuwa da rashin iya tunani na Alzheimer Disease a Turance da sauran cututtukan da su kan addabi tsoffafi. Sakamakon nazari ya shaida mana cewa, fama da ciwon bakin ciki a lokacin da aka tsufa ya kan kara barazanar kamuwa da ciwon Alzheimer har kusan sau 4. Tsoffafin da suke fama da ciwon bakin ciki su kan yi bakin ciki, kuma ba sa son yin mu'amala da mutane. Masu karatu, idan iyayenku ko kuma dangoginku suka nuna alamar hakan, sai ku yi taka tsan-tsan, kila sun kamu da ciwon bakin ciki.

Mistan Wang ya kara da cewa, bai kamata tsoffi masu fama da ciwon bakin ciki su daina shan magani ba, duk da ba sa cikin bakin ciki, zai fi kyau su tsawaita lokacin shan maganin bisa shawarar likita.

Masu juna biyu da matan da suka haihu ba da dadewa ba fa? Wang Gang ya yi nuni da cewa, masu ciki da matan da suka haihu ba da dadewa ba suna cikin matakin musamman a rayuwarsu. Ban da matsin lamba a zaman rayuwa da ayyukan, su kan fuskanci sauyawar jiki da tunani, su kan gamu da matsalar tunani. Ko da yake yanzu mutuwar 'yan tayi da jarirai sabbin haihuwa dukkansu sun ragu sosai a Beijing, har adadin ya yi kasa da na kasashen masu sukuni, karin masu ciki da wadanda suka haihu ba da dadewa ba na fama da matsalar tunani.

Wang Gang ya yi bayani da cewa, kamar yadda aka yi jinyar sauran masu fama da ciwon bakin ciki, a kan yi jinyar masu ciki da kuma wadanda suka haihu ba da dadewa ba ta hanyoyin ba su magani, yin magana da masana masu ilmin halin dan Adam da dai sauransu. Idan ana cikin bakin ciki, zai fi kyau a yi magana da masana ilmin halayyar dan Adam tukuna. Amma idan bakin ciki da ake fama da shi ya tsananta, dole ne a je a ga likitoci masu ilmin halayyar dan Adam. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China