in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawara daga mai sauraro
2016-01-26 15:25:00 cri
Zai yi kyau, idan kuka kirkiro da wani saban shiri mai suna 'muhimman guraren tarishi da yawan shakatawa a kasar Sin'. Saban shirin zai bada babban zarafi ga milyoyin masu sauraronku a fadin duniya da masu san sanin tarishin muhimman guraren tarishi da na yawan shakatawa da bude idanu na kasar Sin, kana shirin zai kara ilmi da wayin kai ga mu masu sauraro bisa sanin muhimman gurare na tarishi da yawan shakatawa na kasar Sin. Banda wannan, shirin zai dunga gabatar mana da tarishin kasar Sin baki dayanta tare da yin bitar irin muhimman gudumowar da magabatan kasar Sin suka bayar wajen gina sabuwar kasar Sin ta zamani.

Dud da cewar, akwai tsoffin shugabannin kasar Sin da suka taka muhimmiyar rawa sosai wajen gina sabuwar kasar Sin ta zamani tare da daura kasar Sin da jama'ar kasar Sin bisa turba ta gari wato bisa salon tsari mai nagarta ga harkokin tafiyar da harkokin gwamnati da samar da walwala mai inganci ga jama'ar kasar Sin, yana da kyau ku kara wayin kai da ilmi ga mu masu sauraro bisa tarishi da gudumowar da madugun gina sabuwar kasar Sin Mao Zadang ya bayar wajen gina sabuwar kasar Sin ta zamani da jama'arta wanda har kawo yanzu al'ummar Sinawa suke ci gaba da tunawa da jagorancin kwarai da marigayi Mao Zadeng ya yi a zamanin rayuwarsa.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China