Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri gare ku, da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya a nan birnin Kano.
Bayan haka, ina farin cikin shaida mu ku cewa, na ji dadin kallon sabon shirin ku na faya fayan bidiyo mai taken 'Tafiya mabudin ilimi' wanda ku ka fara gabatar da shirin farko da na biyu, kuma yanzu haka na riga na koyi wasu kalmomin Sinanci guda 2 wato 'ao yu hui' da 'bing', sai dai kuma ba mu koyi wasu jumloli na Sinanci daga wadannan kalmomi biyu ba. Dangane da haka, ina bayar da shawara ga sashen Hausa da ya fara koya mana yadda ake hada jumla ta Sinanci daga sabuwar kalmar da za mu koya a sabon shiri na gaba. Wannan zai kara taimaka wa masu sauraro wajen saurin koyon harshen na Sinanci.
Ban da wannan, ina kuma bayar da wata shawara dangane da shirya wasa kwakwalwa sai biyu ko sau hudu a kowacce shekara dangane da kalmomi ko jumla ta Sinanci da a ka koyar cikin shirin 'Tafiya mabudin ilimi'.
Da fatan kun fahimta kuma za ku yi duba ga wadannan shawarwari nawa da idanun basira. Na gode.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria