Jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayinda yake tsokaci adangane da bankin raya kasa na kasashen yankin Asia(AIIB) a birnin Beijing na kasar Sin, ya alamunta matsayin karfin jarin kudade isassu da bankin ke da su wanda hakan zai bada zarafi ga bankin ta yadda zai dunga gogaiya da sauran manyan bankunan kasa da kasa da bankunan bada lamani na Imf, Bankin duniya da dai sauran bankuna manya a dud duniya. Muna fata bankin zai ci gaba da samun habakar hada-hadar kudade tare da bada babbar gudumowa wajen aiwatar da aiyukan raya kasa ga daukacin kasashen yankin Asia da ma kasashen duniya baki daya, amin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.