Dud da cewar, cri Hausa kun bada babban zarafi ga masu sauraro a shirye-shiryenku na masamman da kuka watso mana bisa tarishi da karin haske adangane da rayuwar yan kabilar Hui masu bin addinin musulunci dake rayuwa a jihar Ningxia ta kasar Sin. Amma dai yana da kyau ku kara ba wa mu masu sauraro sukunin kara samun ilmi da wayin kai bisa tarishin rayuwar yan kabilar Hui masu bin addinin musulunci. Bayan jihar Ningxia, akwai wasu lardina ko jihohi dake ake samun musulmai yan kabilar Hui a duk fadin jamhuriyar jama'ar Sin?. Su yan kabilar Hui menene sana'arsu, noma da kiwo ko kuma sake-saken kayaiyaki?. Banda wannan, ina so ku kara mana wayin kai bisa tarishin jihar Mangolia ta cikin gida, ko menene gaskiya cewar, mazauna jihar Mangolia ta cikin gida kasar Sin yan asalin kabilar kasar Mangolia ne?. Jihar Mangolia ta cikin gida kasar Sin tayi iyaka da kasashe nawa?. Ko kasashen Sin da Mangolia sun taba gabza yaki a zamanin Da can!?
Daga malam Ali Buuge kiraji Gashua, jihar Yobe, Nigeria.