in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Amurka ta bai wa masu juna biyu da kananan yara shawarar kara cin kifi yadda ya dace
2015-06-24 15:25:35 cri


Kwanan baya, gwamnatin kasar Amurka ta kaddamar da wani daftarin shawara, inda ta bayyana cewa, kamata ya yi masu juna biyu, wato iyaye mata wadanda suke shayar da jariransu, ko matan da suka shirya samun ciki, da kananan yara, su kara yawan kifi da suke ci yadda ya dace.

Hukumar kula da abinci da magani ta kasar Amurka wato FDA, da hukumar kiyaye muhalli ta kasar ne suka bayyana hakan, duba da yadda a shekaru 10 da suka gabata, karin shaidu na kimiyya suka nuna cewa, akwai tarin sinadarin furotin mai inganci, da sinadaran bitamin iri-iri, da sauran sinadarai, da wani nau'in pufa na OMEGA-3 a cikin naman kifi. Kaza lika akwai sinadarin bitamin D a cikin naman wasu kifaye.

Don haka cin naman kifi yadda ya kamata, na da matukar muhimmanci ga masu juna biyu, da iyaye mata wadanda suke shayar da jariransu, ko matan da suka shirya samun ciki, da kananan yara a cewar kundin shawarwarin.

Bisa tanade-tanaden da ke cikin daftarin shawarar, an ce, ya fi kyau masu juna biyu, da dai makamantansu, su ci naman kifi da yawansa ya kai giram 227 zuwa giram 340 a ko wane mako.

A cikin wata sanarwarta, hukumar kula da abinci da magani ta kasar Amurka ta FDA ta ce, shekara da shekaru, ana hana masu juna biyu masu yawa su ci kifi, ko kuma akan kayyade yawan kifin da za su iya ci. Har ma akan hana kananan yara su ci kifi, ko kuma a kayyade yawan kifi da za su iya ci. Amma sabon nazarin kimiyya da aka yi ya nuna cewa, watakila hakan zai iysa sa masu juna biyu da kananan yara su rasa abubuwa masu gina jiki da suke da matukar muhimmanci gare su a fannin girma da kuma kasancewa cikin koshin lafiya.

Amma duk da haka, wannan daftarin shawara da hukumar kula da abinci da magani ta kasar Amurka ta FDA, da hukumar kiyaye muhalli ta kasar suka gabatar, ya yi bayani da cewa, kamata ya yi a kaucewa cin kifin shak, da kifin tilefish da ke rayuwa a sassan mashigin tekun kasar Mexico, da kifin swordfish, da kifin mackerel, saboda sinadarin mercury da suke dauke da shi a jikin su. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China