in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shan koko na taimakawa tsoffi da masu matsakaitan shekaru wajen kare lafiyar kwakwalwarsu
2014-10-27 07:58:16 cri

Masu nazari daga kasar Italiya sun gabatar da sakamakon nazarinsu a cikin mujallar kiwon lafiya mai suna Hypertension, inda suka tantance wasu tsoffi masu shekaru fiye da 90 a duniya wadanda suka kamu da ciwon MCI wato ciwon mantuwa da bai yi tsanani ba. Wadannan tsoffi suna fama da matsalar tuna wasu abubuwa, yin magana, yin tunani da tsai da kuduri. A cikin makonni takwas da masanan suka shafe suna tantance su, an raba tsoffin zuwa rukunoni 3, wadanda suka sha abin sha mai yawan koko, da mai matsakaicin koko da abin shan da ke da koko kadan, a kokarin tabbatar da tasirin da wasu sinadarai da ke cikin koko suka yi kan lafiyar tsoffin. Sakamakon nazarin ya shaida cewa, a jarrabawar da aka yi bayan nazarin, tsoffin da suka sha koko da yawa sun fi wadanda ba su sha koko da yawa ba a fannonin mai da hankali kan wani abu da dai sauransu.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, wasu sinadarai masu kyau da ke cikin koko na taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye da kyautata lafiyar zuciya, haka kuma suna agazawa mutane wajen kare lafiyar kwakwalwarsu. Duk da haka sun yi gargadi da cewa, watakila ba ko wane mutun ne da ke fama da ciwon MCI shan koko zai taimaka masa.

Bayan haka kuma, masu nazarin sun ce, ba tilas ba ne ko wane mutum ya ci cakulan a ko wace rana kasancewar cakulan cike yake da mai da kuma zafi.

Ko yin hakan zai yi tasiri ga hana tsofan kwakwalwar mutane? Masu kimiyya da dama suna ganin cewa, akwai bukatar a ci gaba da nazari kan tasirin cakulan ga kwakwalwa. Yanzu, abu mai muhimmanci shi ne, kamata ya yi a lura da cewa, wannan nazari bai nuna cewa, shan koko a ko wace rana zai taimaka wajen yin rigakafin kamuwa da ciwon MCI ko ciwon Alzheimer ba. Ana bukatar gudanar da wani nazari na dogon lokaci.

A halin yanzu likitocin kasar Amurka sun ba da shawarar cewa, shan koko kadan a ko wane mako na da amfani sosai wajen motsa jikin mutane. Amma duk da haka a sha koko kadan kuma yadda ya kamata. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China