in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana iya kashe kwayoyin cutar Ebola ta hanyoyi da dama
2014-09-21 16:45:42 cri

A yau shirin na mu zai gutsirawa mai sauraro ne sakamako na wani nazari da aka gudanar, wanda ke tabbatar da cewa kwayoyin cutar Ebola kan kama mutane ta cikin kowane irin yanayi da suka kasance ciki, wato alal misali a yanayin wuri maras laima, ko bushasshen wuri kwayoyin cutar suna iya kasancewa makale a tufafi, ko zanen gado tsahon sa'o'i da dama, ta yadda wanda ya yi amfani da wadannan kayayyaki daga baya ka iya kamuwa da cutar.

Kaza lika a yanayi mai danshi, ko lema, ko a yanayi mai sanyi, kwayoyin cutar na kara tsahon lokacin da suke iya kasancewa a raye. Alal misali, idan yanayin zafin jiki ya sauka zuwa digiri 4, kwayar cutar na iya kasancewa a raye har tsahon kwanaki 5 za kuma ta iya kama mutane. Kana kwayoyin cutar na iya rayuwa tsahon lokaci mai yawa, idan yanayi ya yi sanyi har kasa da digiri 70 a kasa da sifiri.

To amma fa bincike ya nuna cewa ana iya kashe kwayoyin cutar ta Ebola cikin sauki. Domin kuwa masana sun nuna cewa, idan zafin yanayi ya kai digiri 60, aka kuma yi awa daya ana lalata karfin kwayoyin cutar dake kama mutane, to ba za su iya kama mutane ba. Sa'an nan in an dafa kwayoyin cutar cikin ruwa mai zafin digiri 100, to za su mutu.

Haka zalika ana iya kashe kwayoyin cutar da magunguna na ruwa, na kashe cututtuka masu dauke da Chlorine, da Alcohol da Phenol, kana ana iya kashe su da hasken Ultraviolet Rays da hashen Heat Rays.

Masanan sun jaddada cewa, tushen kwayoyin cutar ta Ebola na kama mutane su ne gawawwakin dabbobi, ko gawawwakin majiyyata. Haka kuma taba majiyyata masu dauke da cutar kai tsaye, ko taba abubuwan dake dauke da ruwan jikin su, kaar jininsu ko tufafin da suka taba sanyawa, ko zanen gado, ko bargo da suka taba amfani da shi na iya sanya mutane kamuwa da cutar.

Sai dai da wuya ne kwayoyin cutar su yadu ta hanyar numfashin mutane, hakan dai ya nuna cewa kwayoyin cutar Ebola ba sa yaduwa ta hanyar numfashi, ko iskar da mutane ke shaka, wadda hakan hanya ce ta saurin yada cututtuka.

Baya ga haka kuma, dangane da damuwar mutane ta kamuwa da cutar Ebola yayin da suke bulaguro, masanan sun yi bayanin cewa, idan mutum bai taba abubuwa masu ruwa-ruwa kamar yawu, ko fitsari, ko bayan gidan mutanen da kai tsaye ke dauke da cutar ba, ba za ka kamu da ita yayin da kake tafiye-tafiye ba. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China