Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, na yi nazarin gyaran dokar gudanar da aikin gwamnati da hukumomin Beijing suka zartar a kokarin da ake yi na kakkabe hannun manya da kananan jami'an gwamnati daga hada hadar cin hanci da karbar rashawa.
Gyaran dokar da ya biyo bayan shawarwarin da aka cimma yayin cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na JKS da aka gudanar a wannan wata na Oktoba ya burge ni matuka, sakamakon yadda wakilan suka yi la'akari da yadda manyan jami'an gwamnati kan yi amfani da mukamansu wajen kaucewa fuskantar hukunci tare da hana doka ta yi aikinta wajen aiwatar da kwaskwarima ga kudin tsarin mulki.
Hakika, wannan ya bayyana yadda a koda yaushe shugabannin JKS a kasar Sin ke sara suna duban baki gatari, wato suna bibiyar al'amuran gwamnati sau da kafa da nufin aiwatar da gyara a inda ya dace.
Koda yake, babu wanda zai musanta cewa kasar Sin ta riga ta yi suna wajen daukan tsauraran matakai kan jami'anta dake yi wa doka kafar ungulu, amma duk da haka suna ci gaba da aiwatar da kwaskwarimar doka sakamakon yadda masu aikata laifuka kan yi amfani da sababbin dabaru a kullum.
A baya bayan nan dai, komar gwamnatin kasar Sin ta yi nasarar kama wani babban jami'in soja mai suna Zhutai Ho bayan da ya jima yana karbar na goro wajen karawa jami'an soja mukamai ba bisa ka'ida ba. Wannan ya burge ni matuka, saboda a zahirin gaskiya a nan kasashen mu na Afirka doka ba ta cika yin aiki kan manyan jami'an soja ba komai irin munin laifin da suka aikata.
Wani abu da ya kara burge ni da gyaran doka a kasar Sin shi ne, yadda hukumomi suka rage yawan laifukan da a kan zartarwa da hukuncin kisa, sakamakon yadda sannu a hankali batun kare 'yancin bil Adam ke samun ci gaba a kasar ta Sin. Ko shakka babu, wannan zai zama wata kyakkyawar amsa ga masu fafutukar kare hakkin dan Adam da suka dade suna yin suka ga kasar Sin ta wannan fanni.
Dangane da haka, ya zama wajibi a yaba wa hukumomin birnin Beijing bisa yadda suke kwatanta adalci wajen nuna halin ba sani ba sabo ga kowanne dan kasa, muddin ya aikata ba daidai ba.
Shawara dai a nan ita ce, ya dace shugabannin Afirka su rika koyi da kasar Sin wajen zartar da hukuncin doka ga manyan jami'an gwamnati, ba wai ga talaka kawai ba, kamar yadda mu ka saba gani a yanzu.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon-Dabo, Nigeria