in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Murnar cika shekaru 10 da kafuwar kwalejojin Confucius
2014-10-01 16:43:11 cri
Zuwa ga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa da fatan alheri gare ku, ina kuma fatan baki dayan ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, makasudin wannan wasika tawa shi ne bayyana farin cikin dangane da cikar shekaru 10 da kafa kwalejojin Confucius a fadin duniya, musamman bukukuwa masu armashi da aka shirya a harabar kwalejojin dake sassa daban daban na duniya ranar Asabar 27 ga watan Satumban nan.

Hakika, idan aka yi duba ga kokarin yada al'adun Sinawa masu ban sha'awa da kwalejojin Confucius su ka yi cikin shekaru 10, to za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu. Sakamakon irin aikace aikacen kwalejin na fadakar da al'ummar duniya tarihi da al'adun Sinawa, an samu ci gaba mai yawa sosai wajen fahimta tare da karbar al'adun na Sinawa a duk fadin duniya. Har ila yau, bisa kokarin kwalejin mutanen kasashen ketare da ke iya magana ko rubutu cikin harshen Sinanci sun karu matuka. Wannan ya yi tasirin gaske wajen daga darajar kasar Sin har ma da al'adunta a duk duniya.

Koda yake kasar Sin tana da nisan gaske, har ma a na yi mata taken bangon duniya, amma duk da haka, kwalejin Confucius ta kusanto da kasar Sin mai nisa kusa da kasashe tamkar makotanta. Wato, duk wani dalibi da ke halattar kwalejin Confucius to zai gane wa idanunsa wasu al'adun Sinawa wanda a zamanin baya sai an ziyarci kasar Sin ake iya gani. Ga misali, a bikin na bana da aka nuna ta tashar talbijin ta kasar Sin wato 'CCTV News' daya daga cikin kwalejojin ta gayyaci wata Basiniya sanye da rigar Qi Pao, inda ta yi wasa da daya daga cikin fitattun kayan kidan gargajiya na Sinawa bisa tarihi, wato Guzheng. Hakika, wannan ya kayatar da bakin da suka halarci bikin.

Dangane da wannan ci gaba, ina fatan nan gaba kasar Sin za ta kafa kwalejin Confucius a jihar Kano domin mu samu damar kara faimtar tarihi da al'adun Sinawa.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Sent from my Nokia phone

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China