in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muna taya gwamnatin jamhuriyar Jama'ar Sin da al'ummar Sinawa murnar cikon shekaru 65 da kafuwar kasar Sin ta zamani
2014-10-01 16:41:55 cri

Babu shakka, shugabannin kasar Sin na farko kawo na yanzu, sun nuna halin bujunta da kishin kasar Sin wajen aiwatar da aiyukan raya kasa mai yawan gaske, al'amarin da ya kara ingiza bunkasuwar kasar Sin ta zamani. Tarishin kafuwar kasar Sin ta zamani ba zai kammalu ba, har sai an hada da tarishin gwarazon shugabannin kasar Sin na da wayanda suka nuna gwazo da himma ainun wajen aiwatar da muhimman aiyukan masamman da har abada sinawa ba za su taba mantawa da su ba a rayuwarsu. Madugun gina Sabuwar kasar Sin ta zamani malam Mao Zadeng ya yi mulkin adalci da nagarta sosai a zamanin mulkinsa wanda hakan ya zama wani muhimmin batu a tarishin kasar sin kuma babban abun koyi da har abada al'ummar Sinawa ba za su manta da su ba. Har kawo yanzu, sinawa na ci gaba da cin moriyar mashahuran shugabannin kasar Sin da suka yi kaurin suna a zamanin mulkinsu wajen gina sabuwar kasar Sin irinsu, marigayi madugun gina sabuwar kasar Sin ta zamani malam Mao Zadeng da malam Jiang Zemin, Li Peng, Wu Banguo, Li Landging, Zeng Qinghong da Guoqiang da kuma malam Xi Jinping da Li Keqiang da dai sauran mashahuran shugabannin kasar Sin da suka nuna kwazo da himma wajen gina sabuwar kasar Sin ta zamani. Dan haka, muna iya cewa, sabuwar kasar Sin ta zamani da al'ummar sinawa sun samu yalwatuwa da bunkasuwa a dukkan fannonin ci gaban kasa a cikin shekaru 65 da kafuwar sabuwar kasar Sin ta zamani, al'amarin da ya kara ingiza bunkasuwar kasar Sin ta zamani tare da samun nasarar kara hada kan sinawa guri daya. Kana yankunan kasar Sin sun samun muhimman ci gaba sosai yadda yakamata. Tsibirin Diaoyu da Taiwan da yankunan Masamman na Hongkong da Macao da shanghai duk wasu bangare ne dake karkashin ikon mallakar kasar Sin ta zamani kuma wayannan tsibirai da yankuna na kasar Sin sun samun kyautatuwa da ci gaba mai yawan gaske kawo yanzu da al'ummar sinawa ke shagulgulan murnar kafuwar kasar Sin shekaru 65 da kafuwa.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China