in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinadarin bitamin E ko sinadarai masu gina jiki ba su taimakawa wajen rigakafin ciwon zuciya da ciwon kansa
2014-08-24 14:57:42 cri

Kungiyar kula da ba da hidimar yin rigakafi ta kasar Amurka ta kaddamar da wani rahoton kimantawa a kwanan baya, inda ta nuna cewa, sinadarin bitamin E ko sinadarin beta-carotene ba su taimaka wa mutanen da ke cikin koshin lafiya wajen yin rigakafin ciwon zuciya da ciwon kansa.

Kungiyar kula da ba da hidimar yin rigakafi ta Amurka, wata kungiya ce mai zaman kanta, wadda shahararrun likitoci da masana kimiyya suka kafa, wadda kuma ke samun goyon baya daga gwamnatin Amurka. Wannan kungiya ta tantance nazarin da aka yi kan sinadarin bitamin E da sauran sinadarai masu gina jiki a kasar ta Amurka a cikin shekaru 10 da suka gabata, inda suka gano cewa sinadarin na bitamin E ba shi da amfani wajen yin rigakafin ciwon zuciya ko ciwon kansa, haka kuma sinadarin beta-carotene kan sanya mutanen da suke fuskantar barazanar kamuwa da cututtukan su fuskanci karin barazanar kamuwa da ciwon kansar huhu.

Manazartan sun kara da cewa, ba bu isassun shaida da ke nuna cewa, shan nau'o'i daban daban na sinadaran bitamin dake dauke da sinadari mai gina jiki, ko sinadarin abinci masu gina jiki mai kunshe da nau'o'i daban daban, ka iya taimakawa wajen yin rigakafin ciwon zuciya ko ciwon kansa. Amma duk da haka kamata ya yi masu juna biyu su sha sinadarin bitamin nau'in Folic acid bisa shawarar likitoci. Sa'an nan kuma ya kamata tsofaffi su sha sinadarin bitamin D, domin kara karfin kashinsu.

Har wa yau kuma, kungiyar ta ba da shawarar cewa, ya fi kyau mutane su ci nau'o'in abinci masu amfani ga jiki, su ci 'ya'yan itatuwa, kayayyakin lambu, hatsi da danginsa, da ma abincin madara maras sanya kiba, ko mai sanya kibar amma 'yar kadan, da kuma kayan abincikan ruwa da dama. A cewar su irin wadannan abinci suna iya gina jikunan mutane sosai, tare da rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya da ciwon kansa.

Bisa kididdigar da mahukuntan kasar Amurka suka samu, an ce, kusan rabin Amurkawa baligai, suna shan sinadarai masu gina jiki a ko wace rana. Watikila suna bukatar sake tunanin game da ci gaba da shan irin wadannan sinadarai ko a'a.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China